Akalla mutane takwas, ciki har da babban jami’in dan sanda da dan banga aka hallaka a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.
Abdul-Rahman Isah dai shi ne kwamandan rundunar leken asiri ta IRT, wanda aka kashe tare da wani jami’in tsaro na ‘yan banga Hassan Mohammed.
Lamarin dai ya faru ne a a unguwar Kwoi da ke karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Ubah Ogaba ya tabbatar da faruwar lamarin, yayin wani jawabi da ya gabatar a birnin Jos.

