Home Labaru Harin Tegina: Daliban Islamiyya 6 Sun Mutu A Hannun ‘Yan Bindiga

Harin Tegina: Daliban Islamiyya 6 Sun Mutu A Hannun ‘Yan Bindiga

47
0
Daliban Islamiyya

Rahotanni na cewa, shida daga cikin daliban makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko da ke Tegina a jihar Neja sun mutu a hannun ‘yan bindigar da su ka sace su.

Shugaban makarantar Abubakar Alhassan, ya ce ‘yan bindigar sun kira shi domin sanar da shi mutuwar yaran.

Ya ce ‘yan bindigar sun shaida ma shi cewa, yaran sun mutu ne sakamakon rashin lafiya, sannan sun bukaci a yi gaugawar biyan kudin fansar sauran daliban.

Mutumin da ya dauki Naira miliyan 30 zuwa wurin barayin Kasimu Barangana, ya ce an ajiye yaran a wurare 25 cikin dajin da ke dauke da dubban ‘yan bindiga masu dauke da makamai.