Home Coronavirus Kula Da Majinyata: Mu Na Kashe Naira 4,500 Ga Kowanne Mai Cutar...

Kula Da Majinyata: Mu Na Kashe Naira 4,500 Ga Kowanne Mai Cutar Korona – Gwamna Bauchi

727
0
Kula Da Majinyata: Mu Na Kashe Naira 4,500 Ga Kowanne Mai Cutar Korona - Gwamna Bauchi
Kula Da Majinyata: Mu Na Kashe Naira 4,500 Ga Kowanne Mai Cutar Korona - Gwamna Bauchi

Gwamnatin jihar Bauchi ta ce ta na kashe Naira 4,500 domin ciyar da kowanne mai cutar Coronavirus da ke cibiyar killace masu cutar a jihar.

Shugaban kula da harkokin lafiya a matakin farko na jihar Rilwanu Muhammad ya sanar da haka ga manema labarai, sannan ya ce gwamnan jihar Bala Muhammad ne ya bada umarnin ba masu fama cutar isashen abinci.

Wasu daga cikin masu dauke da cutar ta corona sun yi zanga – zanga domin nuna rashin jin dadin su a kan yadda aka barsu kara zube, sai dai  Rilwanu Muhammad ya ce gwamna ya ce a kula da majinyatan sun ji tamkar a gida su ke.

Muhammad ya ce, Gwamna Bala Muhammad ya ce a rika kashe Naira 1,500 a kowanne kwanon abinci da za a ba mai fama da cutar da ke cibiyar killacewa, ma’ana karin kumallo, da abincin rana da kuma na dare, wanda hakan zai bada jimillar Naira 4,500 ga kowanne mutum a duk rana