Home Labaru Sojin Sama Sun Kashe ‘Yan Bindiga 400 A Zamfara Da Katsina

Sojin Sama Sun Kashe ‘Yan Bindiga 400 A Zamfara Da Katsina

1995
0
Tsaro: Sojin Sama Na Naijeriya Sun Kashe ‘Yan Bindiga 400 A Zamfara Da Katsina – DHQ Hedkwatar tsaro ta Nijeriya ta ce rundunar Operation Hadarin Daji ta halaka sama da ‘yan bindiga 200 a jihohin Zamfara da Katsina. Shugaban sashen yada labarai na hedkwatar Major Janar John Enenche ya tabbatar da haka a cikin wata takarda da ya fitar, inda ya kara da cewa rundunar ta kuma ci gaba da kakkabe sauran ‘yan bindigan da ke yankin. Haka kuma, ya ce an kashe ‘yan bindiga a kalla 200 a sansanin ‘yan bindiga da ke Mai Bai a karamar hukumar Jibia da kuma Kurmin Kura da ke Zurmi a jihar Zamfara a tsakanin ranakun 22 da 23 na watan Mayu. Enenche ya cigaba da cewa, an kai samamen ne da jiragen yaki bayan an samu tabbacin cewa, wuraren biyu sun kasance maboyar ‘yan bindigar kuma adanar shanun sata. Kawo yanzu dai, shugaban rundunar sojin sama na Nijeriya ya bada umarnin kara tura kayan aiki zuwa jihohin Kaduna da Neja daNasarawa da Kogi, domin dakile duk wani harin ‘yan bindigan.

Hedkwatar tsaro ta Nijeriya ta ce rundunar Operation Hadarin Daji ta halaka sama da ‘yan bindiga 200 a jihohin Zamfara da Katsina.

Shugaban sashen yada labarai na hedkwatar Major Janar John Enenche ya tabbatar da haka a cikin wata takarda da ya fitar, inda ya kara da cewa rundunar ta kuma ci gaba da kakkabe sauran ‘yan bindigan da ke yankin.

Haka kuma, ya ce an kashe ‘yan bindiga a kalla 200 a sansanin ‘yan bindiga da ke Mai Bai a karamar hukumar Jibia da kuma Kurmin Kura da ke Zurmi a jihar Zamfara a tsakanin ranakun 22 da 23 na watan Mayu.

Enenche ya cigaba da cewa, an kai samamen ne da jiragen yaki bayan an samu tabbacin cewa, wuraren biyu sun kasance maboyar ‘yan bindigar kuma adanar shanun sata.

Kawo yanzu dai, shugaban rundunar sojin sama na Nijeriya ya bada umarnin kara tura kayan aiki zuwa jihohin Kaduna da Neja daNasarawa da Kogi, domin dakile duk wani harin ‘yan bindigan.