Shugaban rundunar sojin kasa na Nijeriya Laftanal Janar Yusuf Buratai, ya ce dakarun sa sun kasahe mayakan kungiyar Boko Haram da na ISWAP dubu 1 da 15 a cikin makonni shidda da su ka gabata.
Buratai ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabi a taron da rundunar Ofireshon LAFIYA DOLE ta gudanar a garin Maiduguri, tare da cewa sun kama manyan mayakan Boko Haram 84 tare da ‘yan leken asirin kungiyar da ma wasu kayayyaki.
Haka kuma, Buratai ya ce dakarun sojin Nijeriya sun kara kaimi wajen yaki da ‘yan Boko Haram da ISWAP, matakin da ya ba su damar samu nasarar wargaza sansanin su da kashe su da dama.
You must log in to post a comment.