Home Labaru Tsaro: Shugaban Rundunar ‘Yan Sanda Ya Gana Da Gwamnan Zamfara

Tsaro: Shugaban Rundunar ‘Yan Sanda Ya Gana Da Gwamnan Zamfara

199
0
Mohammed Bello Matawalle, Gwamnan Jihar Zamfara
Mohammed Bello Matawalle, Gwamnan Jihar Zamfara

Matsalar tsaro ta sa shugaban  rundunar ‘yan sanda na kasa, Muhammad Adamu, ya yi ganawar siri da gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun na jihar Zamfara a gidan gwamnati dake Gusau .

MUHAMMAD ADAMU SHUGABAN RUNDUNAR ‘YAN SANDA TA KASA DA GWAMNAN JIHAR ZAMFARA

A jawabin sa gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun yayi kira ga Shugaban kasa Muhammad Buhari  da ya goyi bayan sulhu da mahara ga gwamnanin arewa maso yamma. dan mu anan Zamfara  mun samu nasarori dadama sakamakon sulhun da mukayi da su maharan.

Ya ce idan har gwamnatin tarayya ta marawa shirin sulhu da aka kirkiro da shi a jahohin, Sakkwato da Katsina da Nija da Kaduna, zai habaka dawamamen zamana lafiya a yanki.

Gwamna Matawalen ya kara da cewa, tu ni gwamnatin sa ta kafa matsuguni uku a yankunan ‘Yan Majalisar Datawa ga Fulani, wanda zai bunkasa rayuwar su.

A nasa jawabin Sufetan ‘Yan sandan Muhammad Adamu, ya ce , sun yi ma Zamfara dirar mikiya ne dan tattanawa da masu ruwa da tsaki ,akan harkar tsaron jihar da iyayan alumma Sarakuna .

Muhammad Adamu ya roki iyayan alumma Sarakuna da su tainaka masu wajan yaki da suke da ‘Yan ta’ada , dan ganin ankawo karahe wannan ta’addancin.