Home Labaru Kujerar Sanata: Hukumar Zabe Ta Ce Zaben Dino Da Smart Bai Kammala...

Kujerar Sanata: Hukumar Zabe Ta Ce Zaben Dino Da Smart Bai Kammala Ba

484
0

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta ce zaben kujerar dan majalisar dattawa na mazabar Kogi ta Yamma bai kammala ba.

Malamin zaben da ya bayyana sakamakon zaben ya ce, kuri’un da aka soke sun fi yawan kuri’un da Adeyemi Smart ya lashe zaben da shi.

Adeyemi Smart na jam’iyyar APC dai ya fi yawan kuri’u a zaben, inda ya samu kuri’u dubu 80 da 118, yayin da Sanata Dino Melaye na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u dubu 59 da 548.

Sai dai malamin zabe ya bayyana cewa, an samu matsaloli a rumfunan zabe 53 da ke da yawan wadanda su ka yi rajista dubu 43 da 127, lamarin da ya sa ba za a iya bayyana Smart a matsayin wanda ya yi nasara ba. Hukumar zabe, ta ce za a sake zabe a wadannan mazabu da aka soke zabukan su, don haka za ta bayyana ranakun da za a gudanar da sabon zabe