Home Labaru Ibtila’i: Mutane 5 Sun Mutu Yayin Da Tankar Mai Ta Kama Da...

Ibtila’i: Mutane 5 Sun Mutu Yayin Da Tankar Mai Ta Kama Da Wuta A Kogi

705
0

Akalla mutane biyar su ka hallaka a wani hatsarin tanka da ya afku a kewayen yankin Felele, hanyar babban titin Abuja zuwa Lokoja.

Wata tankar mai cike da fetur da ta fito daga Lagos ce ta samu ballewar birki, inda ta turmushe wasu motoci biyar a babban gidan mai na NNPC a Felele da ke jihar Kogi. Tuni dai lamarin ya yi sanadiyar barkewa zanga-zanga a tsakanin matasan yankin.