Home Labaru Ilimi Tsaro: Malamin ABU Sun Kubuta Daga Hannun ‘Yan Ta’adda A Kaduna

Tsaro: Malamin ABU Sun Kubuta Daga Hannun ‘Yan Ta’adda A Kaduna

523
0

Malamin jami’ar Ahmadu Bello Adamu Chonoki da kanen sa Umar Chonoki da shi ma malami ne a kwalejin kimiya da fasaha ta Kaduna, sun kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane da su ka tsare su kwanaki da dadewa.

Kakakin kungiyar ‘yan jihar Kebbi mazauna garin Kaduna kuma Garkuwan Wakilin sarkin Zuru Garba Mohammed ya bayyana  haka, inda ya ce Adamu da Umar sun isa fadar sarkin Zuru da misalign karfe 11:15 na safiyar Lahadin da ta gabata.

Idan dai ba a manta ba, kwanakin baya ne masu garkuwa da mutane su ka yi garkuwa da Adamu, inda su ka bukaci iyalan shi su biya kudin fansa har Naira miliyan 2 da babur daya.

Kanen Adamu, wato Umar ne ya kai masu kudaden, sai dai bayan sun kudin kudin sai  shi ma su ka tsare shi, inda su ka bukaci ‘yan’uwan sa su aika da karin naira miliyan 10 kafin su sake su gaba daya.

Har yanzu dai Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna bai ce komai game da kubutar mutanen ba.

Leave a Reply