Home Labaru Kotu Ta Amince Da Belin Sowore Kan Naira Miliyan 100

Kotu Ta Amince Da Belin Sowore Kan Naira Miliyan 100

159
0
Kotu Ta Amince Da Belin Sowore Kan Naira Miliyan 100
Kotu Ta Amince Da Belin Sowore Kan Naira Miliyan 100

Wata babbar kotu da ke Abuja ta amince ta bada belin mai ikirarin yin juyin juya hali a Nijeriya, Omoyele Sowore da mai goya masa baya bisa ra’ayin sa Olawale Bakare wadanda ake tsare da su bisa laifin kokarin aiwatar da manufar juyin juya hali a Nijeriya.

Mai shari’a Ijeoma Ojukwu ta umarci Sowore ya samar da wanda zai tsaya masa a kan zunzurutun kudi Naira miliyan 100 domin karbar belin sa, shi kuma Bakare ya samu mai tsaya masa a kan naira miliyan 50.

Haka kuma kotun ta bukaci dukkan su su zauna a birnin Abuja, sannam su tabbatar sun nisanta kan su daga dukkan wata zanga-zanga.

Idan dai za a iya tunawa, Sowore na tsare ne tun lokacin da aka kama shi a jihar Legas bisa jagorantar zanga-zangar da ya yi wa lakabi  da juyin juya hali a Nijeriya.