Hukumar kwastan ta kasa ta ce, ta kama motoci 1,072 da wasu kayayyaki da gwamnati ta hana shigowa da su a jihar Katsina.
Sannan Hukumar ta kama wadannan motoci ne a daidai ‘yan fasa kwaubri kea kokarin shigo da su Nijeriya ta barauniyar hanya.
Kakakin hukumar Joseph Attah ya tabbatar da kamen a ranar Juma’ar da ta gabata a garin Katsina, sannan ya ce sun kuma kama buhunan shinkafa 19,000 da jarkokin fetur 4,765, da bindigogi da dama da kuma buhunan takin zamani NPK 131.
Ya ce gwamnati ta rufe iyakokin Nijeriya ne domin hana aiyukkan ‘yan fasa kwaubri da shigowar mutanen da ba ‘yan Nijeriya ba.
Attah ya yi kira ga mutane da su guji siyan kayan da ‘yan sumogal suka shigo da su, tare da cewa yin haka na gurguntar da tattalin arzikin kasan.
Idan
ba a manta ba a ranar Talatar da ta gabata ne shugaban Hukumar Kwastan, Hamid
Ali, ya bayyana cewa, rufe iyakokin Najeriya alheri ne mai dimbin ya wa ga Niajeriya.