Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 9 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 9 A Zamfara

1184
0
‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 9 A Zamfara
‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 9 A Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe wasu sojoji 9 a kauyen sunke da ke karamar hukumar Anka a jihar Zamfarakamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rahoton ya nuna cewa, ‘yan bindigna sun je kauyen Sunke a babura ne inda suka rika harbin sojoji da ‘yan sanda.

Majiya daga gwamnatin jihar, ta sanar da jaridar cewa, harin da ‘yan bindigar suka kai, martani ne ga kisan ‘yan ta’addan da sojoji suka yi.

Har ila yau majiyar ta ce, sojoji sun kashe wasu ‘yan ta’adda da suka tuba, suka kuma yi alkawarin maida martani.

Tubabbun ‘yan ta’addan sun turo ‘yan uwan su ne, inda suka afkawa sojoji a kauyen  A ranar Larabar da ta gabata.

Wannan harin dai,  ya biyo bayan ta sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar cewa,  akwai yuwuwar ‘yan Boko Haram su kai hari a kananan hukumomi 7 da ke jihar Zamfara.

Mai magana da yawun rundunar Operation Hadarin Daji da ke jihar Captain Oni Orisan ya yi alkawarin kara tattaunawa a kan faruwar lamarin.

RAHOTO- ADAMAWA