Wata babbar kotu da ke Abuja ta amince ta bada belin mai ikirarin yin juyin juya hali a Nijeriya, Omoyele Sowore da mai goya masa baya bisa ra’ayin sa Olawale Bakare wadanda ake tsare da su bisa laifin kokarin aiwatar da manufar juyin juya hali a Nijeriya.
Mai shari’a Ijeoma Ojukwu ta umarci Sowore ya samar da wanda zai tsaya masa a kan zunzurutun kudi Naira miliyan 100 domin karbar belin sa, shi kuma Bakare ya samu mai tsaya masa a kan naira miliyan 50.
Haka kuma kotun ta bukaci dukkan su su zauna a birnin Abuja, sannam su tabbatar sun nisanta kan su daga dukkan wata zanga-zanga.
Idan
dai za a iya tunawa, Sowore na tsare ne tun lokacin da aka kama shi a jihar Legas
bisa jagorantar zanga-zangar da ya yi wa lakabi da juyin juya hali a Nijeriya.