Home Labaru Korafin Zabe: Mu Na Da Shaidu Sama Da 400 A Kan Zaben...

Korafin Zabe: Mu Na Da Shaidu Sama Da 400 A Kan Zaben Shugaba Buhari – PDP

342
0

Jam’iyyar PDP, ta ce ta na da shaidu sama da 400 da za ta gabatar a gaban Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa, inda ta ke kalubalantar zaben da aka bayyana Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya yi nasara.

Babban Lauyan PDP Levi Uzeugwu ya bayyana haka, yayin da ya ke amsa tambayoyin mai shari’a Mohammed Garba.

Uzeugwu ya kara da cewa, sai dai kuma idan har za su iya samun sararin gabatar da shaidu 300 daga cikin tulin wadanda su ke da su, wannan zai iya sa su tabbatar da hujjojin da su ke dauke da su da kuma sake nazarin matsayin su.

Alkalin kotun, ya bukaci lauyan ya yi la’akari da tulin yawan hujjoji ko shaidun da ya ce ya na dauke da su, domin kotu ta ji saukin bada lokacin yadda bangarorin za su yi nazarin wadannan shaidu.