Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kebbi, ta ce ta yi nasarar kama bata-gari 32, da masu garkuwa da mutane 10, da kuma wasu da ke hada baki da masu garkuwa da mutane guda uku.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Garba Danjuma ya bayyana wa manema labarai haka a makon da ya gabata, inda ya ce rundunar ‘Operation Puff Adder’ ce ta kama mutanen tsakanin watannin Mayu da Yuni.
Ya ce sun kama mutanen dauke da bindigogi, da wayoyin Komfutoci, da igiyoyin wutar lantarki, da wukake da kuma adduna, kuma an fara ne da masu hada baki da masu garkuwa da mutanen ne a karamar hukumar Wasagu.
Kwamishinan ya kara da cewa, sauran mutanen da su ka kama sun aikata laifuffukan da su ka hada da fashi da makami, da satar babura, da fyade da kuma yawo da makamai a jikin su, kuma da zarar an kammala bincike za a gabatar da su a gaban kotu.