Home Labaru Ilimi Wata Sabuwa: Jarabawar Sai Da Katin Zama Dan Kasa – JAMB

Wata Sabuwa: Jarabawar Sai Da Katin Zama Dan Kasa – JAMB

1446
0

Hukumar shirya jarrabawar share fagen shiga jami’a JAMB, ta ce daga yanzu babu dalibin da zai kara yin rijistar zana jarrabawa ba tare da ya mallaki lambar katin zama dan kasa ba, ta na mai cewa, wannan sabon tsari ne kuma zai fara aiki daga shekara ta 2020.

Shugaban sashen yada labarai na hukumar Dakta Fabian Benjamin ya sanar da haka, inda ya ce daliban da hukumar bada katin zama dan kasa ta ba lambar tantamncewa ne kawai za su iya yin rijista domin rubuta jarrabawar JAMB.

Dakta Fabian ya bayyana haka ne, yayin da ya ke jawabi a wajen taron kara wa juna sani da hukumar shirya jarrabar kammala karatun sakandare NECO ta shirya a garin Keffi na jihar Nasarawa.

Mista Benjamin, ya ce hukumar JAMB ta kammala shiri da hukumar bada katin zama dan kasa don tabbatar da sabon tsarin ya fara aiki a shekara mai zuwa. Ya ce yin hakan, ya na daga cikin kokarin hukumar JAMB na dakile makudin jarrabawa ta hanyar sojan-gona da musayar bayanan masu rubuta jarrabawa.