Home Labaru Korafin Zabe: Kotu Ta Wanke Jami’an Tsaro Daga Zargin Magudin Zabe

Korafin Zabe: Kotu Ta Wanke Jami’an Tsaro Daga Zargin Magudin Zabe

187
0

Kotun Daukaka Kara ta yi watsi da zargin da jam’iyyar PDP ta yi wa jami’an tsaro cewa sun yi magudi domin Shugaba Muhammadu Buhari ya kada Atiku Abubakar a zaben shekara ta 2019.

Haka kuma, Kotun ta yi watsi da wani bangare da jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa APC ta yi amfani da jami’an tsaro, inda su ka hada kai su ka yi walle-walle da zaben shugaban kasa na shekara ta 2019.

Biyo bayan korafin da jam’iyyar PDP ta gabatar, hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta nuna wa kotu cewa kamata ya yi PDP ta bayyana sunayen jami’an tsaron da ta ke zargi a cikin karar ta da shigar. Don haka kotu ta tsame jami’an tsaro daga cikin wadanda ake zargi.