Home Labaru Almundahana: Gwamnatin Tarayya Ta Kwato Naira Biliyan 900 Na Aikin Mazabu –...

Almundahana: Gwamnatin Tarayya Ta Kwato Naira Biliyan 900 Na Aikin Mazabu – Radda

190
0

Babban sakataren kwamitin da ke ba shugaban kasa shawara akan yaki da rashawa Farfesa Sadiq Radda, ya ce gwamnatin tarayya ta dawo da kimanin naira biliyan 900 na aikin mazabu daga wasu ‘yan majalisar dokoki ta tarayya.

Radda ya bayyana wa manema labarai haka ne a wajen taron yaki da rashawa da ya gudana a Maiduguri, inda ya ce kudin an ba sanatoci da ‘yan majalisar wakilai ne domin aiwatar da ayyuka a mazabun su.

Sai dai ya nuna da-na-sanin cewa wasu ‘yan majalisar sun sace kudaden, amma hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta kwato su.

Farfesa Radda, ya ce kwamitin zai bayyana duk gwamnan da ya lakume kudade da sunan tsaro, domin babu gwamnan da zai ci bulus ta hanyar fakewa da tsaro.