Home Labaru Wata Sabuwa: An Kama Wani Soja Da Aka Tura Yakin Boko Haram...

Wata Sabuwa: An Kama Wani Soja Da Aka Tura Yakin Boko Haram Ya Na Fashi A Yola

565
0

Wani jami’in Soja da ke kan aiki ya shiga hannun hukuma, bisa zargin yi wa wata mata fashi da makami, wanda ya kamata a ce ya na bakin daga a Garin Munguno domin yakar ‘yan ta’adda.

Bayan gabatar da Sojan tare da wani mutum da ake zargi da fashi a Garin Yola, Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Adamawa DSP Sulaiman Nguroje, ya ce mutanen sun aikata laifin ne a Ranar Talatar da ta gabata da tsakar dare, inda su ka tare wata mata su ka yi mata fashin mota kirar Toyota Camry a kan titi.

DSP Nguroje, ya ce an yi dace wani Jami’in ‘yan sanda da ke aiki a lokacin ya kai kara, inda nan take aka shiga aiki tare da hadin kan ‘yan banga aka kama mutanen da ake zargi da aikata mummunan aikin.

Kakakin ya ce, sun karbo motar, da kuma bindiga samfurin AK-47 da carbi 35 na harsasai daga ‘yan fashin, sannan daga bisani an gano cewa Dampa Hyellambamun Soja ne da aka tura aiki a Monguno, sai dai jami’in Sojin ya ce, yunwa ce ta kama shi har ta kai ya na neman ya ci babu.