Home Labaru Kin Jinin Baki: Jirgi Zai Debo ‘Yan Nijeriya Daga Afirka Ta Kudu

Kin Jinin Baki: Jirgi Zai Debo ‘Yan Nijeriya Daga Afirka Ta Kudu

176
0
Geoffrey Onyeama, Ministan Harkokin Wajen Nijeriya
Geoffrey Onyeama, Ministan Harkokin Wajen Nijeriya

An yi wa ‘yan Nijeriya mazauna kasar Afirka ta Kudu tayin jirgin sama kyauta domin dawowa gida, bayan barkewar rikice-rikicen nuna kin jinin baki kamar yadda ma’aikatar harkokin kasashen wajen Nijeriya ta bayyana.

Ma’aikatar ta ce, mamallakin kamfanin jiragen sama na Air Peace ya ce zai bada jirgi kyauta a kwaso ‘yan Nijeriya aranar Juma’a mai zuwa.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, ta ce ‘yan Nijeriya da ke sha’awar dawowa gida na iya tuntubar ofishin jakadancin Nijeria a biranen Pretoria da Johannesburg domin shirye-shiryen da su ka dace.

Harin da aka kai wa shaguna da wuraren sana’a na baki a kasar Afirka ta Kudu dai ya tunzura ‘yan Nijeriya da dama da ke ganin ba a yi adalci ba.

Ministan harkokin wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama ya shaida wa manema labarai cewa, bayanan da ya samu sun nuna cewa ba a kashe dan Nijeriya ko guda a rikicin ba.