Home Labaru Difilomasiyya: Afrika Ta Kudu Ta Rufe Ofishin Jakadancin Ta A Nijeriya

Difilomasiyya: Afrika Ta Kudu Ta Rufe Ofishin Jakadancin Ta A Nijeriya

209
0
Ofisoshin Jakadancin, Kasar Afirka Ta Kudu Da ke Nijeria
Ofisoshin Jakadancin, Kasar Afirka Ta Kudu Da ke Nijeria

Kasar Afirka ta Kudu ta sanar da rufe ofisoshin jakadancin ta da ke biranen Abuja da Lagos, biyo bayan hare-hare da tarzomar ramuwar gayya a kan kadarorin ‘yan kasar da su ka auku sakamakon hare-haren kin jini da ’yan kasashen waje ke fuskanta a Johannesburg.

Kakakin ma’aikatar horkokin wajen Afrika ta Kudu Lunga Ngqengelele, ya ce, bayan sun samu rahotanni da barazana daga wasu ‘yan Nijeriya, sun yanke shawarar rufe ofisoshin jakadancin su, yayin da su ke ci-gaba da nazari a kan yadda al’amura ke tafiya.’

Ya ce shawarar dakatar da ayyukan na zuwa ne bayan wasu gungun matasa sun yi kokarin balle ofishin jakadancin su da ke Lagos.

An dai shiga zaman tankiya ta fuskar diflomasiya tsakanin kasashen biyu, bayan Nijeriya ta ayyana bijire wa taron tattalin arziki na duniya a birnin Cape Town na kasar Afrika ta Kudu.