Home Labaru Ambaliya: Gonaki 3000 Da Gidaje 120 Ne Su Ka Salwanta A Jihar...

Ambaliya: Gonaki 3000 Da Gidaje 120 Ne Su Ka Salwanta A Jihar Jigawa

492
0

Akalla gonaki 3000 da gidaje 120 ne su ka salwanta sakamakon ambaliyar ruwa da ta afka wa garin Zugo da ke karamar hukumar Guri ta jihar Jigawa.

Jami’in hulda da jama’a na karamar hukumar Sanusi Doro ya bayyana haka, inda ya ce sai da aka nemi matasa su ka rika cika buhunna da kasa su na toshe hanyoyin ruwa.

Ya ce ambaliyar da aka yi ta wanke manyan tituna da su ka hada da babban titin Una zuwa Zugobia, lamarin da ya sa ba a iya jigilar kayan gona zuwa kasuwanni da kuma shiga gonaki.

Doro ya yi kira ga Hukumar Samar da Agajin Gaugawa ta jihar, su taimaka wa mutanen da su ka tafka hasara sanadiyyar ambaliyar da aka yi.