Home Labaru Duba Lafiya: Burin Mu Ya Cika Kan Jagoranmu Elzakzaky- Kungiyar IMN

Duba Lafiya: Burin Mu Ya Cika Kan Jagoranmu Elzakzaky- Kungiyar IMN

190
0

Kungiyar mabiya akidar ‘yan Shi’a a Najeriya ko kum Islamic Movement Of Nigeria ta ce abinda ta dade ta na gwagwarmaya ya tabbata, bayan fitar jagoranta na ta neman magani zuwa kasar Indiya.

Sheikh Ibrahim Zakzaky da matan sa

Sheikh Ibrahim Zakzaky ya tafi kasar Indiya domin neman magani kuma ya tashi ne daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja, inda kungiyar ta ce ta jingine duk wata zanga-zanga a yanzu.

Wakilin kafar yada labarai ta BBC ya ce jami’an tsaro sun ki ba shi damar ganin malamin, amma wani wakilin gidan talabijin na NTA, ya ce ya hango lokacin da ake sa malamin a cikin jirgin saman kamfanin Fly-Emirates.

Rahotanni sun ce malamin zai fara yada zango ne a birnin Dubai, kafin daga bisa ya wuce kasar Indiya, inda zai yi jinya a asibitin Medanta.

Sai dai an yi kokarin jin bakin kwamishinan karkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan bai amsa kiran waya ba.

 A farkon wannan watan ne shugaban kungiyar Izala ta Najeriya Shaikh Abdullahi Bala Lau da kuma Shaikh Ahmad Gumi suka ce ya kamata gwamnati ta yi wa jagoran ‘yan Shi’a Shaikh Ibrahim Zakzaky adalci.