Home Labaru Kasafin Kudin 2020: Buhari Zai Bayyana Gaban Majalisun Dokoki A Ranar Talata...

Kasafin Kudin 2020: Buhari Zai Bayyana Gaban Majalisun Dokoki A Ranar Talata Mai Zuwa

393
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 a zauren Majalisar Dokoki ta Kasa, a wani zama na hadin gwiwa a tsakanin majalisar wakilai da ta dattawa.

Bayanin haka na kunshe ne a cikin wata wasika da fadar shugaban kasan ta aike wa shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

A cewar wasikar, shugaban kasa ya nemi a amince da karfe biyu na rana ya zama lokacin gabatar da kasafin kudin na badi.

Idan ba a manta ba, majalisar ta amince da tsarin kudaden da za a kashe na musamman bayan ta kara adadin su daga Naira Tiriliyan 10,002 zuwa Naira Tiriliyan 10,729.4, wato an samu karin sama da Naira Biliyan 700.