Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 a zauren Majalisar Dokoki ta Kasa, a wani zama na hadin gwiwa a tsakanin majalisar wakilai da ta dattawa.
Bayanin haka na kunshe ne a cikin wata wasika da fadar shugaban kasan ta aike wa shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.
A cewar wasikar, shugaban kasa ya nemi a amince da karfe biyu na rana ya zama lokacin gabatar da kasafin kudin na badi.
Idan ba a manta ba, majalisar ta amince da tsarin kudaden da za a kashe na musamman bayan ta kara adadin su daga Naira Tiriliyan 10,002 zuwa Naira Tiriliyan 10,729.4, wato an samu karin sama da Naira Biliyan 700.

