Home Labaru Kashi 90 Na Motoccin Najeriya Ta Barauniyar Hanya Aka Shigo Da Su-Ali

Kashi 90 Na Motoccin Najeriya Ta Barauniyar Hanya Aka Shigo Da Su-Ali

319
0
Kashi 90 Na Motoccin Najeriya Ta Barauniyar Hanya Aka Shigo Da Su-Ali
Kashi 90 Na Motoccin Najeriya Ta Barauniyar Hanya Aka Shigo Da Su-Ali

Shugaban hukumar Kwastam ta Najerita, Kanal Hameed Ali mai ritaya ya ce kashi 90 cikin 100 na motocin da ke Najeriya ta haramtaciyyar hanya wasu hatsabiban mutane suka shigo da su.

Shugaban hukumar Kwastam ta Najerita, Kanal Hameed Ali

Hamid Ali, ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a Abuja.

Ya ce jami’an hukumar sa suna kai sumame wuraren sayar da motocci ne cikin ‘yan kwanakin nan domin tabbatar da cewa motoccin da ke wuraren ta halastaciyyar hanya aka shigo da su.

A cewar sa, Najeriya na bukatar kudin shiga domin yin ayyukan cigaba hakan yasa ya zama dole a karba haraji a kan motoccin da aka shigo da su ba bisa ka’ida ba. “

Muna son muyi amfani da wannan damar mu tabbatar da cewa dukkan motoccin da ke kasar mu son bi ta hannun kwastam wanda hakan ke nufin an biya musu haraji. “

Muna neman kudaden shiga daga ko ina sai kuma ga wasu mutane da ke shigo da motocci amma ba su son biyan haraji. “

Abinda muke yi yanzu, muna zartar da dokar kasa ne kawai wadda ya bamu damar karbar haraji a madadin gwamnatin Najeriiya tare da tabbatar da cewa motoccin da ni da kai zamu siya suna da inganci kuma suna da takardu na ainihi,” inji shi