Home Labaru Sanata Ibrahim Shekarau Ya Yi Wa Jam’iyyun Siyasa Kudin-Goro

Sanata Ibrahim Shekarau Ya Yi Wa Jam’iyyun Siyasa Kudin-Goro

329
0
Sanata Ibrahim Shekarau, Dan Majalisar Dattawa Kuma Tsohon Gwamnan Jihar Kano
Sanata Ibrahim Shekarau, Dan Majalisar Dattawa Kuma Tsohon Gwamnan Jihar Kano

Dan majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Ibrahim Shekarau, ya bayyana duk jam’iyyun siyasa a matsayin miyagu, domin duk kundin tsarin dokokin su na dauke ne da manufofi iri guda.

Shekarau ya bayyana haka ne, yayin da ya ke jawbai a wajen bikin cikar Nijeriya shekaru 59 da samun yancin kai, wanda cibiyar Hudaibiyya ta shirya a Kano.

Ya ce bambancin ya ta’allaka ne a kan wanda k ake tarayya da shi, da dalilan da su ka sa ka ke tarayya da shi, domin duk jam’iyyun siyasa su na fadin abubuwan da su ka yi kamanceceniya da juna ne.

Sanatan ya kara da cewa, da a ce ‘yan Nijeriya su na da zabin samar da nagartaccen shugaba mai kula, da ba su riki dimokradiyya a matsayin mafita ba.