
Kungiyar dalibai ta Najeriya NANS ta yi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi gaggawar sa baki game da ƙarin kuɗin makaranta da jami’o’i ke shirin yi tun kafin hakan ya janyo matsaloli a faɗin Najeriya.
Sakataren ƙungiyar na ƙasa Usman Baba Kankia, ya shaida wa BBC cewa duk makarantun gwamnatin tarayya sun ƙaƙƙara kuɗaɗe fiye da kashi 250 cikin dari, to sai dai Sakataren ƙungiyar ya ce suna zargin cewa makarantun sun samu umarnin ƙara kuɗin makarantar ne daga sama.
Ya ce dalilin ya da sa kenan suka rubuta wasika ga shugaban ƙasa, inda suka buƙace shi a matsayin sa na uba, ya sa baki domin mayar da kuɗin makarantar yadda yake a baya.
Wasu jami’o’in dai sun bayyana cewa sun yi ƙarin kuɗin makarantar ne domin samun damar gudanar da makarantun na su.
You must log in to post a comment.