Home Home Aikin Zabe: INEC Za Ta Dauki Masu Yi Wa Kasa Hidima Da...

Aikin Zabe: INEC Za Ta Dauki Masu Yi Wa Kasa Hidima Da Ke Da Bukata Ta Musamman

29
0
Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu, ya tabbatar wa masu yi wa ƙasa hidima da ke da lalurar buƙata ta musamman cewa hukumar za ta ɗauke su aikin babban zaɓen da ke tafe.

Farfesa Mahmood Yakubu, ya tabbatar da haka ne a lokacin da ya jagoranci tawagar kwamishinonin hukumar zuwa shalkwatar masu yi wa ƙasa hidima da ke nan Abuja.

Ya ce INEC hukuma ce da ke bayar da daidaito ta fuskar ɗaukar ma’aikata, tana ba ‘yan ƙasa dama ba kawai ta jefa ƙuri’a ba, har da aikin zaɓe ba tare da la’akari da yanayin da suke ba, kamar masu larura ta musamman, za a ba su dama wajen gudanar da aikin zabe.

Shugaban hukumar ta INEC ya kuma yaba wa hukumar yi wa ƙasa hidimar kan taimakon da take ba hukumar zaɓen cikin shekaru masu yawa.

Ya yi alƙwarin ci gaba da aiki da yarjejeniyar da ke tsakanin hukumar sa da hukumar yi wa ƙasa hidimar, tare da alƙawarin kare lafiyar masu yi wa ƙasa hidimar a lokacin gudanar da zaɓen.