
Kungiyoyin kare hakkin ‘yan jarida sun yi kira ga hukumomin Sudan ta Kudu su saki wasu ‘yan jarida shida da suka tsare bayan ɓullar wani faifan bidiyo da ya nuna shugaban ƙasar Salva Kiir na yin fitsari a wando yayin wani taro a ƙasar.
Ana zargin ‘yan jaridar da fitar da bidiyon wanda aka ɗauka a wani taro a da shugaban ya halarta a ƙasar.
Bidiyon wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta a watan Disamba ya nuna shugaban ƙasar Salva Kiir na yin fitsarin a wondonsa a daidai lokacin da ake sauraron taken ƙasa a wani taron da aka gabatar a ƙasar.
Daga nan ne kuma aka kama ‘yan jaridar shida waɗanda ma’aikatan kafar yaɗa labaran ƙasar ne a wani abu da ya yi kama da yunƙurin gano wanda ya saki bidiyon.
Ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasar ta yi kira da a saki ‘yan jaridar shida.
A baya-bayan nan ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam na yawan kiraye-kiraye ga hukumomin ƙasar da su daina muzgunawa tare da yin barazana ga ‘yan jarida a ƙasar.
You must log in to post a comment.