Home Labaru Karin Albashi: Ma’aikatan Jiragen Sama Na Nijeriya Sun Jinjina Wa Shugaba Buhari

Karin Albashi: Ma’aikatan Jiragen Sama Na Nijeriya Sun Jinjina Wa Shugaba Buhari

322
0
Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Kungiyoyin ma’aikatan jiragen sama na Nijeriya, sun yaba wa shugaba Muhammadu Buhari, sakamakon sa hannu a kan dokar karin mafi karancin albashi na naira dubu 30.

Wata majiya ta ce, kungiyoyin sun bayyana jin dadin su ne a lokacin da su ke zantawa da manema labarai a Legas.

Shugaban gamayyar kungiyoyin Ilitrus Ahmadu, ya ce matakin zai taimaka wajen ci-gaba da kuma kara wa ma’aikata kwarin gwiwar gudanar da ayyukan su.

Ya ce har yanzu naira dubu 30 da aka sanya wa hannu bai kai tsarin kudin albashin ma’aikata na Afrika ba.

Sannan ya nuna tabbacin gwamnatoci na tarayya da jihohi da sauran cibiyoyi za su gaggauta fara aiwatar da sabon tsarin domin kula da walwalar ma’aikata.