Home Labaru Bangar Siyasa: ‘Yan Sanda Sun Samu Makamai A Sakatariyar PDP Da APC...

Bangar Siyasa: ‘Yan Sanda Sun Samu Makamai A Sakatariyar PDP Da APC A Kano

532
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, ta samu wasu makamai a sakatariyar jam’iyyar PDP da ke karamar hukumar Tudun Wada, da kuma sakatariyar jam’iyyar da ke Kano APC.

Haka kuma, an kama ‘yan bangan siyasa takwas da ke da nasaba da makaman kamar yadda jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan DSP Haruna Abdullahi ya bayyana.

DSP Abdullahi, ya ce makaman sun hada da takubba da adduna, da wukake, da miyagun kwayoyi iri-iri da sauran makamai masu hadari da ‘yan bangan siyasa ke amfani da su.

Ya ce kamun da kuma samo makaman, ya biyo bayan mamayar da ‘yan sanda ke kaiwa a mafakar masu laifi a jihar Kano.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas, ya ce babu wani dan jam’iyyar APC da ke da nasaba da makaman da aka samu.

Sakataren jam’iyyar PDP Shehu Wada Sagagi kuwa cewa ya yi, babu wanda ya kai rahoton lamarin sakatariyar jam’iyyar na jihar Kano, ya na mai tabbatar da cewa an saki ‘yan jam’iyyar PDP da aka kama akan beli, yayin da ‘yan sanda ba su samu komai na laifi tattare da su ba.

Leave a Reply