Gwamnatin tarayya ta fara shirye-shiryen kalubalantar hukuncin da kotu ta yanke na kwace kadarorin najeriya da ya kai na dala billiyan 9.
Mai Shari’a Butcher na kotun kula da harkokin hada-hadar kudade na kasar Burtaniya ya yanke hukuncin a karar da wasu kamfanoni suka shigar.

Jim kadan bayan yanke hukuncin wanda yaba kamfanonin nasara, gwamnatin tarayya ta sha alwashin daukaka kara, wanda take ganin ba a yi mata adalci ba.
A cikin wata sanarwa da ta fito ta ma’aikatar kula da harkokin shari’a, ta ce tuni ta bukaci lauyoyinta su kafa kwamitin daukaka kara akan hukuncin da kotun ta yanke.
You must log in to post a comment.