Home Labaru Samar Da Tsaro: Buratai Ya Yabawa Jami’an Soji

Samar Da Tsaro: Buratai Ya Yabawa Jami’an Soji

153
0

Babban hafsin sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai, ya yabawa jami’an soji bisa namijin kokari da suka yi wajen yaki da ayyukan ta’addanci a jihar Katsina.

Buratai ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun mai rikon mukamin jami’in yada labarai da hulda da jama’a Kanar Sagir Musa.

Kanar Sagir Musa, Kakakin Rundunar Sojin Nijeriya
Kanar Sagir Musa, Kakakin Rundunar Sojin Nijeriya

Sanarwar ta ce Buratai ya yabawa jami’an sojin ne a lokacin da ya ziyarci rundunar yaki da ayyukan ta’addanci mai suna Operation Harbin Kunama da Hadarin Daji a yankin Arewa maso gabas.  

Ya ce rundunar za ta ci gaba da aiki ba dare ba rana, tare da yin abubuwan da za su karawa jami’anta kwarin gwiwar gudanar ayyukansu yadda ya kamata.