Home Labaru Wasanni: FIFA Ta Dakatar Da Siasia Har Abada

Wasanni: FIFA Ta Dakatar Da Siasia Har Abada

285
0

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta dakatar da tsohon mai horas kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Samson Siasia bisa laifin amincewa da sai da wasa.

Siasia ya zamo kocin Najeriya daga shekarar 2010 zuwa 2011 sannan kuma na wani dan lokaci a 2016, sai dai babu tabbas a kan lokacin ya aikata wannan laifin.

Ya kuma taba kasancewa kocin tawagar Najeriya ta ‘yan kasa da shekara 20 da kuma 23.

A wata sanarwa da ta fitar, FIFA ta ce an samu Siasia da laifin amincewa ya karbi na-goro domin sauya sakamakon wasanni.

Wannan mataki yana da alaka da bincike mai zurfi da FIFA ke yi kan halayyar Wilson Raj Perumal, wanda aka samu da laifin sayar da wasa a kasar Singapore.

Shi ne dan Afirka na uku da FIFA ta dakatar dangane da batun na Perumal bayan da aka dakatar da tsohon jami’in kwallon Saliyo Abu Bakarr Kabba da na Botswana Mooketsi Kgotlele a watan Yuli, na tsawon shekara biyar da kuma har abada.

A lokacin da yake buga kwallo, Siasia ya lashe gasar Kofin Afirka a 1994 da Super Eagles, inda ya murza wa kasar leda sama da sau 50, sannan ya ci kwallo 16.