Home Coronavirus An Kirkiro Manhajar Android Na Gwajin Coronavirus

An Kirkiro Manhajar Android Na Gwajin Coronavirus

333
0
Manhajar za ta rika samar da bayanan cutar COVID19 daga Hukumar Lafiya ta Duniyar da kuma Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya.
Masu amfani da manhajar za su iya yi wa kansu gwajin cutar coronavirus ko kai rahoton bullarta.

An kaddamar da manhajar Android da za a yi amfani da ita wurin yaki da annobar coronavirus a jihar Kano.

Ana sa ran amfani da manhajar wadda aka fara gwajinta a ranar Laraba 14 ga Afrilun da muke ciki, domin gwajin cutar da kuma kai rahoton bullarta a jihar Kano ko makwabtanta.

Manhajar za ta kuma rika samar da bayanai da alakaluman cutar kai tsaye daga Hukumar Lafiya ta Duniyar (WHO) da kuma Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya (NCDC).

Masu amfani da manhajar za su iya amfani da ita wurin yi wa kansu gwajin cutar ko kai rahoton cutar ga jami’an lafiya na ko-ta-kwana masu yaki da cutar a jihar.

Kakakin Gwamnan Jihar ya ce mutane ne iya saukar da manhajar mai suna COVID19 KANO GUIDE domin sanyawa a wayoyinsu.