Home Labaru Kiwon Lafiya Mutum 9 Sun Warke Daga Coronavirus A Abuja

Mutum 9 Sun Warke Daga Coronavirus A Abuja

431
0
Mutum 20 ke nan aka sallama bayan sun warke daga cutar coronavirus a Abuja.
Ministan Abuja, Muhammad Musa Bello ya ce yanzu mutum 20 ne suka warke daga cutar coronavirus a Abuja.

An samu karin Mutum 9 da suka warke daga cutar coronavirus a Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja.

An sallami mutum 9 din ne bayan gwajin da aka yi musu bayan killace su da aka yi, ya tabbatar da cewa sun warke, a cewar Ministan Abuja, Muhammad Musa Bello.

Sallamar mutanen da tuni suka koma gidajensu a ranar Laraba 15 ga Afrilun 2020, ya sa yawan wadanda suka warke da cutar COVID-19 a Abuja karuwa zuwa mutum 20.

Abuja ita ce ta biyu wurin yawan masu cutar coronavirus a Najeriya, bayan jihar Legas mai mutum 214.

Daga sadda cutar coronavirus ta fara bulla a Najeriya zuwa yanzu, mutum 58 ne suka kamu da ita a Abuja, cikinsu har da mutum 20 da suka warke.