Home Labaru Zaben Kogi, Bayelsa APC Ce Za Ta Yi Nasara-Tinubu

Zaben Kogi, Bayelsa APC Ce Za Ta Yi Nasara-Tinubu

351
0
APC

Jigo a  Jam’iyya APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce babu makawa jam’iyyar ce za ta lashe zaben gwamnonin jihar Kogi da kuma na Bayelsa da za a gudanar.

Ahmed Tinubu,, Jigo a  Jam'iyya APC, Asiwaju Bola
Ahmed Tinubu,, Jigo a Jam’iyya APC, Asiwaju Bola

Furucin Tinubu na kunshe ne cikin wata sanarwa da ya gabatar a Benin, a yayin  wani taron murnar zagoyowar ranar haihuwar Sarkin Benin Cif David Edebiri.

Ya ce babu shakka tsintsiya ta kasance tambari na jam’iyyar APC, kuma ya nada yakinin cewar  za su ribaci tsintsiya wajen share kurakuren da, jam’iyyar ta yi a baya domin tabbatar da nasarar a zaben jihohin biyu.

Tinubu ya ce, babu abinda ya ke sa rai da fatan gani face nasarar APC a zaben jihar Kogi da Bayelsa domin babu wasu jam’iyyun a jihohin biyu da za su iya ja da ita.

Dangane da korafe-korafen da ake yi na cewar gwamnan jihar Kogi  Yahaya Bello bai kyautawa al’ummar sa ba ta fuskar hidima da kwazon aiki, ya ce dole ne a yi korafi a siyasa domin shi korafi shi ne romon da dimokuradiyya.