Home Ilimi Kakakin Majalisar Wakilai Ya Nemi Afuwa Kan Hotunan Karatunsa A Jami’Ar Amurka 

Kakakin Majalisar Wakilai Ya Nemi Afuwa Kan Hotunan Karatunsa A Jami’Ar Amurka 

359
0

Kakakin Majalisar Wakilai ta kasa Femi Gbajabiamila ya nemi afuwa daga ‘yan kasa saboda wasu hotunansa da ya sanya a shafin tuwita, wadanda ke nuna yana karatu a Jami’ar Harvard da ke Amurka, a lokacin da jami’o’in gwamnati na kasar ke rufe saboda yajin aiki.

Ganin irin caccakar da yake sha kan sanya wannan hoto ganin cewa ga halin da jami’o’in kasar nan ke ciki a rufe sama da wata biyar shi ne ya nemi afuwa

Tun watan Fabrairu jami’o’in gwamnati ke rufe saboda malamai na yajin aiki kan zargin gwamnati da kin cika alkawarin da ta yi a yarjejeniya da suka yi a baya, a game da kudaden alawus da kuma samar da kudi ga jami’o’in.

A ranar Talata ne Kakakin ya sanya hotunan nasa a tuwita inda yake nuna cewa ya koma makaranta yana karatu kan shugabanci.

Har ma yana nuni da cewa, shekaru ko girma ba ya hana karatu.

Leave a Reply