Home Labarai Ta’Addanci: Buhari Bai Ma San An Yi Barazanar Kama Shi Ba Sai...

Ta’Addanci: Buhari Bai Ma San An Yi Barazanar Kama Shi Ba Sai Da Na Gaya Masa – El-Rufa

1
0

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya ce shi ne ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari game da barazanar da masu ikirarin jihadi suka yi cewa za su kama shugaban da shi gwamnan.

Gwamman ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da ‘yan jarida da aka yada kai tsaye a jiya da daddare.

Idan dai ba a manta ba a karshen makon da ya gabata ne masu ikirarin suka fitar da wani biidiyo da ke nuna mutanen da suka sace na jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, tun a watan Maris inda a ciki suke barazanar cewa sai sun kamo shugaban kasar da gwamnan.

El-Rufai ya ce shi Buhari bai ma san da wannan barazana ba sani ba sai da ya gaya masa, sannan kuma Gwamman Jihar Zamfara Bello Matawalle ya kai wa shugaban hoton bidiyon ya gani.

Gwamnan na jihar kaduna ya ce daman shi tun a baya an gargade shi da ya yi hankali shi da iyalinsa a kan wannan barazana.

Gwamnan ya ce ai shi daman tun baya da shekara biyar yake bayar da shawara da a shiga dajin a yi wa sansanoninsu ruwan bama-bamai, da cewa ta hakan ne za a yi maganinsu.