Home Labaru Ilimi Takaddama: Gwamnan Neja Ya Dakatar Da Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya

Takaddama: Gwamnan Neja Ya Dakatar Da Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya

230
0

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya dakatar da Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na jihar, Dakta Isah Adamu.

Sai dai babu wani cikakken bayani game da dalilin da yasa aka dakatar da shi, amma majiyarmu ta tattaro cewar hukuncin na da nasaba da rashin jituwar da ta kunno kai kan batun malaman firamare, yayin da wasu majiyoyin suka ce siyasa ce kawai.

An umarci Daraktan hukumar na uku, Alhaji Abdulkadir Shehu Nafuntua, ya karbi ragamar tafiyar da harkokinta nan take.

Sai dai tuni wasu malaman makaranta a jihar suka shiga dandalin sada zumunta na Facebook suna nuna farin cikinsu kan matakin da Gwamnan ya dauka.

Leave a Reply