Home Labaru Juyin Mulki: Nijeriya Ta Na Sa Ido Bayan Abin Da Ya Faru...

Juyin Mulki: Nijeriya Ta Na Sa Ido Bayan Abin Da Ya Faru a Sudan – Minista

255
0

Gwamnatin Nijeriya, ta ce tana sa ido a kan lamarin da ke faruwa a kasar Sudan, bayan sojoji sun hambarar da Gwamnatin Omar Al-Bashir.

Ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama, ya ce abin da Nijeriya ta damu da shi shi ne, kada a yi rikici kuma a dawo da mulkin dimokradiya nan ba da dadewa ba.

Ya ce har yanzu su na samun labarai a kan abin da ke faruwa, duk da cewa ba su da cikakkun bayanai da alkaluma.

Onyeama ya cigaba da cewa, wannan wani lamari ne da babu cikakken bayani a kan yadda manyan sojojin da su ka jagoranci juyin mulki a Sudan za su mika mulki ga farar hula.

Jami’an tsaro a kasar dai tuni su ka bayyana cewa, hambarar da Al-Bashir tare da sa dokar hana fita za su sama masu lokaci kuma a kawo karshen zanga-zangar.

Leave a Reply