Home Labaru Harin Ta’Addanci: An Kashe Akalla Mutane 10 a Jihar Benue

Harin Ta’Addanci: An Kashe Akalla Mutane 10 a Jihar Benue

222
0

A kalla mutane 10 su ka hallaka, a wani hari da aka kai kauyen Vaase da ke karamar hukumar Ukum ta jihar Benue.

Wata majiya ta ce an kai wa mutanen da ke zaune a kan iyakar jihohin Benue da Taraba ne harin.

Mai ba gwamnan jihar Benue shawara ta fuskar tsaro Kanar Paul Hemba, ya ce ya samu rahoton cewa an kashe mutane tsakanin 8 zuwa 10 a harin, kuma wadanda su ka kai harin sun hada da ‘yan kabilar Jukun da kuma makiyaya.

Hemba ya ce lamarin ya faru duk da irin kokarin da gwamnatin jihar Benue ta ke yi na kawo karshen rikici a fadin jihar.

A karshe ya roki mutanen kauyen su kwantar da hankulan su, ya na mai cewa hukuma za ta dauki mataki akan lamarin.

Rahotanni sun ce akalla gidaje 100 aka kone, yayin da sama da mutane 3,000 ‘yan kabilar Tiv da ke jihar Taraba sun kaurace wa gidajen su zuwa jihar Benue da garuruwan da ke makwaftaka da jihar.

Leave a Reply