Home Labaru Juyin-Juya-Hali: Sowore Ya Ce Ba Gudu Ba Ja Da Baya

Juyin-Juya-Hali: Sowore Ya Ce Ba Gudu Ba Ja Da Baya

161
0

Dan jarida kuma mai fafutuka Omoyele Sowore da hukamar tsaro ta farin kaya SSS ta kama, ya yi kira ga ‘yan NIjeriya su cigaba da zanga-zangar neman sauya halayyar gwamnati.

Sowore ya bayyana haka ne ga abokan gwagwarmayar sa da su ka kai ziyara wurin da ya ke tsare.

A safiyar ranar Litinin da ta gabata, masu zanga-zangar Juyin-Juya-Hali  su ka fantsama a kan titunan wasu jihohi domin fara gudanar da gangamin su, wanda su ka shirya yi na tsawon  kwanaki, sai dai da alama abubuwa ba su faru yadda su ka so ba.

Mai magana da yawun hukumar DSS ya bayyana cewa, su ke da alhakin kama Sowore, kuma dalilin su na yin hakan shi ne, zargin da ake yi ma shi na yunkurin hambarar da gwamnatin Nijeriya.

Omoyele Sowore dai ya yi takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata, kuma shi ne ya shirya zanga-zangar da ya so ta mamaye jihohi 21 na Nijeriya.
)�)