Home Labaru Belin El-Zakzakky: Hukumar DSS Ta Amince Da Umurnin Kotu

Belin El-Zakzakky: Hukumar DSS Ta Amince Da Umurnin Kotu

246
0

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ta ce za ta bi umurnin kotu na ba Sheikh Ibrahim El-Zakzaky damar tafiya kasar waje domin samun kulawar likitoci.

Idan dai ba a manta ba, a safiyar Litinin da ta gabata ne, babbar kotun jihar Kaduna ta ba El-Zakzakky da matar sa Zeenat beli domin zuwa neman magani a kasar waje.

Da ya ke yanke hukunci, mai shari’a Darius Kobo ya yi umurnin cewa, jami’an gwamnatin jihar Kaduna su yi wa El-Zakzaky rakiya zuwa kasar waje.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Litinin da ta gabata, kakakin hukumar Peter Afunnaya, ya ce kamar yadda ya ke a tsarin hukumar za ta bi umurnin kotun.