Home Labaru Kiwon Lafiya Ambaliya: An Rufe Jami’ar Tafawa Balewa Sakamakon Mutuwar Dalibai 2

Ambaliya: An Rufe Jami’ar Tafawa Balewa Sakamakon Mutuwar Dalibai 2

647
0

Hukumar gudanarwa ta jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, ta ruffe makarantar na tsawo makonni biyu, biyo bayan annobar ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyyar mutuwar daliban ta da dama.

Idan dai za a iya tunawa, wasu adadin dalibai sun mutu yayin da wasu da dama su ka jikkata, a lokacin da wata gada ta rufta sakamakon ambaliyar ruwa a yankin Gubi na Jami’ar.

Wata majiya ta ce dalibai biyu ne su ka mutu, yayin da har yanzu ba a ga wasu da dama ba.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban dalibai na jami’ar Naziru Mohammed, ya ce dalibai biyu ne kawai su ka mutu yayin da wasu biyu su ka jikkata.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Rijistaran jami’ar Dakta AG Hassan, ya umurci dalibai su bar sansanin jami’ar ba tare da bata lokaci ba daga ranar 6 ga watan Agusta.

A cewar sa, daliban za su koma a ranar Litinin, 19 ga watan Agusta, ya na mai mika ta’aziyya da jaje ga iyaye, da daliban makaranta da jami’ar baki daya a kan wannan mummunan lamari.