Home Labaru Joe Biden Na Ci Gaba Da Samun Nasara

Joe Biden Na Ci Gaba Da Samun Nasara

241
0
Joe Biden Na Ci Gaba Da Samun Nasara
Joe Biden Na Ci Gaba Da Samun Nasara

Tsohon Mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ya sake samun gagarumar nasara a zaben fidda gwanin Jam’iyyar Democrat da aka yi a ranar talata a Jihohi 6, matakin da ya say a zamo a sahun gaba wajen kayar da Sanata Bernie Sanders domin kalubalantar shugaba Donald Trump a zaben watan Nuwamba.

Manazarta na ci gaba da bayyana cewa, Joe Biden ya lashe jihohi 9 daga cikin jihohi 14 da suka kada kuri’a a zaben Super Tuesday, domin fida dan takara a Jam’iyyar Democrat.

Biden ya bada mamaki ganin yadda ya sha gaban babban abokin takarar sa, Bernie Sanders a jihar Texas mai muhimmanci, sai dai ana hasashen cewa, Mr Sanders zai yi nasara a California da kuma wasu karin jihohi uku.

‘Yan takarar biyu na kan gaba wajen neman tikitin fafatawa da shugaba Donald Trump a zaben shugaban kasa da za a gudanar a watan Nuwamba mai zuwa.

Tsohon Magajin Garin Birnin New York, Michael Bloomberg ya kashe fiye da rabin Dala biliyan 1 a yakin neman zaben sa, amma bai lashe koda jiha daya ba.