Home Labaru Gwamnati Ta Kara Ma Manyan Ma’aikata Dubu 1 Da Dari 583 Girman

Gwamnati Ta Kara Ma Manyan Ma’aikata Dubu 1 Da Dari 583 Girman

242
0
Albashi: Sai Da Lambar Bvn Za Ku Samu Albashin Ku - Gwamnati
Albashi: Sai Da Lambar Bvn Za Ku Samu Albashin Ku - Gwamnati

Gwamnatin tarayya ta amince da karawa wasu manyan ma’aikatan gwamnati dubu 1 da dari 583 karin girma zuwa matakin darakta.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta samu sa hannun shugaban hukumar ma’aikatan gwamnati Tukur Bello Ingawa, wacce ta ke nuni da karin girma zuwa mataki na 14 da 15 da 16 da kuma na 17.

Idan dai ba a manta ba, a shekara ta 2019 ne hukumar ta gudanar da jarabawar karin girma ga ma’aikatan gwamnati da kuma jami’an kula da sha’anin mulki da ke ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya, domin tsallakar da su zuwa matakai na gaba.

Kakakin hukumar Felicia Eniola ta sanar da sunayen wadanda karin girman ya shafa, mataki da ya nuna muhimmancin da gwamnati ta sa a cigaba domin jin dadin ma’aikata tare da tabbatar da ingancin tsarin aikin gwamnati.