Home Labaru Kama Aiki: Ganduje Ya Ba Sabbin Sarakunan Kano Takardar Kama Aiki

Kama Aiki: Ganduje Ya Ba Sabbin Sarakunan Kano Takardar Kama Aiki

611
0
Kama Aiki: Ganduje Ya Ba Sabbin Sarakunan Kano Takardar Kama Aiki
Kama Aiki: Ganduje Ya Ba Sabbin Sarakunan Kano Takardar Kama Aiki

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya mika takardun kama aiki ga sabon sarkin mai martaba Aminu Ado Bayero da Nasiru Ado Bayero a matsayin sarakunan Kano da na Bichi.

Nadin Aminu Ado Bayero a mtsayin sarkin kano na zuwa ne bayan Gwamna Ganduje ya tube rawanin sarkin Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano a ranar Litinin din da ta gabata.

Haka kuma majiyar ta ce, an nada Nasiru Ado Bayero a mtsayin sarkin Bichi ne saboda cike gurbin da Aminu Ado Bayero ya bari a masarautar.

Da ya ke jawabi jim kadan bayan ya karbi takardar kama aikin a gidan gwamnatin jihar Kano, sabon Sarki Aminu Ado Bayaro ya ce a matsayin sa na musulmi ya yadda da kaddara, domin Allah baya kuskure ko kadan.

Sabon sarki Aminu Bayaro ya cigaba da cewa, wajibi ne su tuna da marigayin tsohon sarki Ado Bayero, wanda ya ce mu kiyaye tare da jin tsoron Allaha koda yaushe, sannan y ace maihaifin su ya  horar da su a kan hakuri da biyayya ga na gaba.

Mai martaba Aminu Ado Bayaro ya yi kira ga al’ummar kano da kasa baki daya su ji tsoron Allah, su kuma kaunaci juna don kawo ci gaba ga masarautar Kano da kasa baki daya.

Leave a Reply