Home Labaru Iftila’i: Mutum Hudu Sun Mutu Bayan Gini Ya Rufto A Delta

Iftila’i: Mutum Hudu Sun Mutu Bayan Gini Ya Rufto A Delta

304
0

A kalla mutane hudu ne suka mutu sakamakon ruftowar wani gini mai hawa uku da ake kan ginawa a garin Abraka da ke karamar hukumar Ethiope ta Gabas a Jihar Delta.

An kuma ruwaito cewar akwai wasu mutane da suka makale a cikin ginin da ya rufto.

Duk da cewar ba a tabbatar da ainihin dalilin da ya janyo ruftawar ginin ba, an gano cewa ginin ya rufta ne yayin da ake ruwa kamar da bakin kwarya a safiyar ranar Asabar din nan .

Wata majiya ta ce wadanda ginin ya ruftowa leburori ne da sauran ma’aikata da suka fake cikin ginin suna jirar ruwan saman ya tsaya su koma aiki.

Mutanen da ke aikin ba su da yawa sosai amma an tabbatar da rasuwar mutane hudu a cikinsu.
��G����@�$�